Firayin ministan kasar Libya mai barin gado Abdullah Thinni, ya bayyana cewa, zai zauna zaman jiran yanke hukunci na kotu kafin mika mulki ga sabon firaministan kasar.
Thinni ya ce, yana da muradin biyayya ga kotu a kan kalubalen da ake fuskanta, to amma ya ce, akwai wata kara da aka daukaka a kotu, kuma a ranar Alhamis za'a yanke hukumnci a kan karan.
Tun farko dai Thinni, ya ki mika mulki ga zababben firaministan Ahmed Maitiq, a inda ya fake da cewar, sakamakon kada kuri'ar majalisar dokokin kasar ya ba da sakamako da suka saba da juna, a inda sai ya nemi shawarar kotu a kan ko yana iya mika mulki, duk da wannan bambanci da aka samu.
Thinni ya ce, yana ci gaba da tuntubar wanda zai gaje shi, Maitiq, kuma babu wani sabani da ya shiga tsakaninsu, to amma kamar yadda ya ce, yanzu matsalar kawai ita ce yadda aka samu rarrabuwar kawuna a majalisar dokokin kasar. (Suwaiba)