Kwamitin tsaro na MDD ya yi kira a kan dukanin bangarori dake adawa da juna a kasar Libya, da su tabbatar da cewar, an gudanar da zaben kasar a cikin kwanciyar hankali, ya kuma jaddada cewar, zaben na da mahimmanci wajen ganin kasar ta samu gwamnatin demokradiyya, wacce za ta maye gurbin gwamnatin rikon kwarya ta kasar.
A bisa tsarin gudanar da zabe na kasar, 'yan kasar Libya mazauna kasashen ketare, su ne suka bude kofar zaben bayan da suka kada kuri'ar zaben sabbin 'yan majalisar a ranar Asabar da ta wuce a kasar ta Libya, an kebe ranar 25 ga watan Yuni ya zama ranar da 'yan kasar za su zabi 'yan majalisar dokoki na kasar.
Wani muhimmin bangare na MDD na ci gaba da sa ido a kan halin da ake ciki a Libya, sai dai kuma MDD na damuwa kwarai a bisa rarrabuwar kai na siyasa da kuma tabarbarewar al'amurran tsaro a kasar, wanda MDD ta ce, dole ne a magance shi ta hanyar farfado da wani tsari na siyasa.
Kwamitin tsaron MDD mai mambobi 15, ya gabatar da kira a kan dukanin kungiyoyi na Libya, wadanda suka dakata da tashin hankali, da su gudanar da wata tattaunawa da juna, domin samar da matsaya guda daya, a game da matakin da za'a dauka a nan gaba da kuma mahimman ababen fifiko da ya wajaba a kan gwamnatin, domin a yi sauyin gwamnati a cikin ruwan sanyi, tare da tabbatar da cewar, kwamitin tsarin mulkin kasar ya yi aikin da ya wajaba a kansa. (Suwaiba)