Kungiyar tarayyar Turai EU ta yi allawadai da babbar murya a ranar Alhamis kan harin bom da ya faru a ranar Laraba a babbar kasuwa dake birnin Abujan Najeriya da ya haddasa mutuwar mutane 21 da jikkata 17.
Wannan harin shi ne na baya baya cikin jerin hare-haren ta'addancin dake cigaba da tada hankalin al'ummar Najeriya, har ma da sace-sace mata da kananan yara a arewa maso gabashin wannan kasa dake yammacin Afrika, in ji kakakin ma'aikatar kungiyar Turai kan harkokin wajen (SEAE).
Masu hannu kan wadannan tashe-tashen hankali, ya kamata su bayyana gaban kotu, kuma ya kamata su sako dukkan mutanen da suka sace, ko suka yi garkuwa da su, in ji wannan jami'in tare da bayyana goyon bayan EU ga gwamnatin Najeriya kan yakin da take da ta'addanci da tashe-tashen hankali. (Maman Ada)