Wani jami'i ya bayyana cewar, nan ba da jimawa ba ne za'a kammala shirye-shirye na maido da Aminu Ogwuche zuwa gida Najeriya daga kasar Sudan a sakamakon zargin da ake yi masa na dasa bam a tashar motocin bas, a Abuja, wanda ya yi sanadiyyar hallaka mutane fiye da 70, tare da raunata wasu da dama.
Jakadan kasar Sudan dake Najeriya, Tagelsir Ali ya shaidawa 'yan jarida a Abuja, babban birnin gwamnatin Najeriya cewar, Sudan da Najeriya suna da matakai masu sharudda da aka tsara, wadanda ake amfani da su wajen maida mutum kasar shi idan ya yi laifi.
An kame Aminu Ogwuche, a Sudan a sakamakon wani kokari na ofishin bangaren leken asiri na sojojin Najeriya, da kuma hukumar 'yan sandan ta kasa da kasa, wacce ke hedkwata a rundunar 'yan sanda ta Najeriya, da kuma hukumomin tsaro na kasar Sudan.
Kamar yadda jakadan na kasar Sudan ya bayyana, akwai yarjejeniya tsakanin Sudan da Najeriya, kuma ya ce, ya kamata a kara duba yarjejeniyar a taron gamayya da kasashen biyu suka yi a Khartoum a kwanan baya. (Suwaiba)