Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, shugaban cibiyar tattara bayanai ta kasar Mike Omeri, ya ce, maharan da suka tada ababen fashewar, sun isa kantin ne kan wasu babura, inda nan take suka tada ababen fashewa kusa da mashigarsa, kafin daga bisani sojoji su yi musu kofar rago.
Mr. Omeri ya ce, jami'an tsaron wadanda suka bude wa maharan wuta, sun hallaka daya, yayin da suka kame dayan da ransa.
Tuni dai ministan birnin tarayyar kasar Dr. Bala Mohammed ya ziyarci wadanda suka samu raunuka sakamakon fashewar a asibitin tarayya dake unguwar Maitama, inda ya ce, gwamnatin tarayyar kasar za ta dauki nauyin jinyarsu.
Wani dan jarida ya bayyana a Abuja cewa, harin da aka kai ranar Laraba a Abuja ya rutsa da editan jaridar New Telegraph mai suna Suleiman Bisalla. (Ibrahim/Saminu)