Wani abu mai kara ya fashe a daf da wani gidan kallon kwallo, yayin da jama'a ke kallon gasar cin kofin duniya a jihar Yobe dake arewa maso gabashin tarayyar Najeriya.
Babban jami'in 'yan sandan yankin Sanusi Rufa'i, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, fashewar ta auku ne a daren ranar Talata yayin da cincirindon jama'a ke tsaka da kallon wasa a birnin Damaturu, fadar mulkin jihar. Ko da yake bai bayyana yawan mutanen da harin ya ritsa da su ba.
Wasu wadanda suka ganewa idanunsu yadda lamarin ya auku, sun ce, sun ji kara mai tsanani, kuma suna zaton harin ya ritsa da mutane da dama. Kana jim kadan da aukuwar hakan, jami'an tsaro sun isa wurin domin gudanar da bincike. (Saminu)