Shugaban kasar Tanzaniya Jakaya Kikwete ya bayyana a kwanan baya cewa, kungiyar hadin gwiwar Tanganyika da Zanzibar a tsawon shekaru hamsin za ta iyar kasancewa wani gwaji domin kafa wata gamayyar sisaya ta kasashen gabashin Afrika,
Mafarkin shugabannin kasashen Afrika na hada kan kasashen Afrika zai iyar zama gaskiya, in ji mista Kikwete a yayin bikin zagayowar cikin shekaru 50 na kungiyar hadin gwiwa tsakanin Tanganyika da Zanzibar a cikin hadaddiyar jamhuriyyar Tanzaniya, da shugabannin kasashen waje da dama suka halarci wannan biki.
Haka kuma ya jaddada cewa, idan hadin gwiwa tsakanin Tanganyika da Zanzibar ya ci gaba a tsawon shekaru 50, to akwai yiyuwar a cimma kafa wata gamayyar siyasa ta kasashen gabashin Afrika da za ta kunshe kasashen Tanzaniya, Burundi, Kenya, Uganda da Rwanda. (Maman Ada)