Rahotanni daga jihar Plateau a tarayyar Najeriya, na cewa, a kalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu, sakamakon harin da wasu dauke da makamai suka kaiwa kauyukan Gako da Tanjol, dake karamar hukumar Riyom.
An ce, maharan sun aukawa kauyukan biyu ne da sanyin safiyar ranar Laraba, inda suka rika budewa mutane wuta, suka kuma kone wasu majami'u guda biyu. To amma sai dai rundunar 'yan sandan yanki ta ce, gawawwakin mutane 6 ta gano bayan aukuwar harin.
Koda yake dai ba a kai ga tantance dalilin wanna hari ba, a hannu guda mazauna yankin na ganin mai yiwuwa ne, ya zamo ramuwar gayya ta dauki ba dadin da kabilun da basa ga maciji da juna ke ci gaba da yi a yankin.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jihar ta Plateau ya ce, an garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa wani asibiti mallakar wata kungiya ta kiristoci. Kaza lika da yawa daga al'ummar yankin sun kauracewa gidajensu, sakamakon tsoron abin da ka iya aukuwa a nan gaba.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta bayyana daukar alhakin kai harin.
Da ma dai jihar ta Plateau ta sha fama da rikice-rikicen kabilanci da na addini, inda a baya bayan nan rashin jituwa tsakanin Fulani makiyaya, da 'yan kabilar Berom masu rinjaye a yankin kudancin jihar, ya yi sanadiyar hallaka mutane da dama, mafiya yawan su mata da kananan yara. (Saminu)