Gwamnatin Najeriya ta bayar da sanarwar kame Kanar Agene Ogwuche mai ritaya, mahaifin mutumin da ake zargi da shirya kai harin bam a tashar mota a Abuja, babban birnin Najeriya, wanda ya haddasa mutuwar mutane sama da 70, kana wasu da dama suka jikkata.
Kakakin hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (SSS) Marylyn Ogar ce ta bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja, ta ce, ana bukatarsa da ya amsa dalilin da ya sa bai kawo 'dan nasa ba, a lokacin da ake bukatar hakan yayin da ya sanya hannu a kan takardar neman belinsa.
Ta kuma ce, hukumar 'yan sandan kasa da kasa ce ta damke daya daga cikin wadanda suka kitsa kai harin, mai suna Abubakar Sadiq Ogwuche, kuma nan ba da dadewa ba za a tuso keyarsa zuwa Najeriya daga kasar Sudan.
An kama Abubakar Sadiq Ogwuche, 'dan Najeriya haifaffen kasar Burtaniya ne a ranar 12 ga watan Nuwamban shekarar 2011 a filin saukar jiragen sama na Nmandi Azikiwe da ke Abuja, yayin da ya iso daga Burtaniya inda ake tuhumarsa da laifin ayyukan da suka shafi ta'addanci, amma aka sake shi a ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 2012, sakamakon matsin lamba daga masu ragin kare hakkin bil-adama.
Yanzu dai an sanya ladan dala 153,000 ga wanda ya taimaka da bayanan da za su kai ga damke Ogwuche da kuma Rufai Abubakar Tsiga. dukkansu 'yan kungiyar Boko Haram da ke zargi da kai hare-haren na Abuja. (Ibrahim)