Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kakkausar suka a kan mumunan harin da aka kaiwa sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar Mali.
Ban Ki-moon, wanda ya fadi hakan a cikin wata sanarwa, kamar dai yadda kakakin babban sakataren na MDD ya bayyana wa manema labarai, ya ce, harin da aka kaiwa sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD MINUSMA a garin Aguelhok a can Mali, ya haifar da kashe wasu sojojin kiyaye zaman lafiya guda hudu, daga kasar Chadi, ya kuma jikkata wasu guda 6, kuma sannan sojoji da yawa na kasar Mali sun sami rauni a harin da aka kai.
Shugaban MDD ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, da kuma gwamnatocin Mali da Chadi, Ban ki-moon ya kuma yi fatan wadanda suka samu rauni za su samu sauki a cikin 'dan lokaci.
Sanarwar ta ce, wannan harin ba zai sa MDD ta dakatar da goyon bayan da take baiwa kasar Mali da jama'arta a kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya mai dorewa a Mali. (Suwaiba)