Hukumar kaura ta duniya IOM, ta gabatar da wani kira na neman agajin dalar Amurka miliyan 97.2, domin ta yi amfani da kudin wajen ci gaba da bayar da agaji a kasar Sudan ta Kudu, nan da zuwa watan Disamba mai zuwa.
Shugaban gudanar da ayyukan hukumar kaura ta duniya, a Sudan ta Kudu, John McCue ya bayyana a cikin wata sanarwa cewar, kiran da hukumar ta yi na neman taimako, ya zama tilas saboda jama'ar Sudan ta Kudu wadanda suka yi kaura fiye da miliyan guda sun shiga wani hali na bukatar taimako na gaggawa.
Hukumar ta ce, karin taimako daga kasashen duniya zai taimaka wajen karawa hukumar kauran ta duniya karfin gwiwa wajen gudanar da ayyukanta. (Suwaiba)