in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tashin hankali ya tsananta a Ukraine
2014-05-04 13:36:15 cri

Tashin hankali ya tsananta a Ukraine, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, wadansu kuma suka jikkata, sannan kuma an saki masu sa ido guda 12 daga kungiyar tsaro da hadin gwiwa na yankin Turai da aka tsare a ranar Asabar din nan 3 ga wata, sakamakon shiga tsakani da kasar Rasha ta yi.

Fada dai ya kaure ne tsakanin magoya bayan gwamnati da masu adawa da gwamnatin a Odessa ranar Jumma'a, inda mutane 43 suka hallaka, wassu 174 kuma suka jikkata, kamar yada gwamnati ta sanar.

A kalla mutane 9 daban sun mutu a kusa da Slavyansk ranar Jumma'ar da ta wuce lokacin da sojojin Ukraine suka tsaurara tsaro a garin, sai dai sun yi asasar jiragen sama masu saukan ungulu guda biyu bayan da aka harbo su lokacin wannan arangamar.

Kasar Rasha ta zargi mahukuntar Ukraine da hannu a cikin wannan aika-aikan a Odessa, tana mai bayanin a jiya Asabar cewa, babu amfanin gudanar da zaben shugaban kasar a cikin halin da ake ciki yanzu na tashin hankali da zaman fargaba.

Shugaba Obama na Amurka a ranar Jumma'a ya ce, kasarsa da Jamus a shirye suke su kakaba takunkumi akan iyaka idan Rasha ba ta daina kawo rudani a Ukraine ba.

Haka kuma a ranar Jumma'ar, kwamitin tsaro na MDD ya kira taron gaggawa karo na biyu a wannan makon domin tattauna halin da ake ciki a Ukraine.

Magatakardar MDD Ban Ki-moon ya jaddada matukar damuwar shi game da tashin hankalin da ake fuskanta a gabashi da kudancin bangaren tsohuwar tarayyar jamhuriyar Soviet, yana mai jaddada cewa, tattaunawa a siyasance shi ne kadai hanyar mafita a cikin wannan tashin hankali. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China