in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira da a yi taka tsan tsan kan batun Ukraine
2014-04-14 14:54:17 cri

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wang Min, ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a rikicin siyasar kasar Ukraine, da su kai zuciya nesa, su kuma dauki matakan hana kara tabarbarewar lamurra a kasar.

Mr. Wang, wanda ya bayyana hakan yayin taron gaggawa da kwamitin tsaron MDD ya gudanar, ya ce, kasar Sin na da burin ganin an magance matsalar da Ukraine ke fuskanta ta hanyar da kowa zai amfana. Ciki hadda daukar matakan diflomasiyya, da rage sabanin dake tsakanin masu ruwa da tsaki, tare da kawo karshen ka ce na ce, cikin ruwan sanyi.

Daga nan dai Wang ya jaddada kudurin kasar Sin, na goyon bayan sauran kasashen duniya, a yunkurin da ake yi na warware wannan matsala ta Ukraine cikin lumana. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China