Karin jirage marasa matuka da sojojin mayakan sama guda 80 a cigaban taimakon da kasar Amurka take baiwa Nigeriya wajen neman yara 'yan matan nan fiye da 200 da aka sace ya koma ayyuka na sararin sama, in ji Steve Warren, kakakin hukumar tsaro ta Pentagon a ranar Alhamis din nan.
Steve Warren a lokacin ganawa da manema labarai ya yi bayanin cewa, jirage marasa matuka da sojojin mayakan sama da aka aika ba a Nigeriya aka kai su ba, an kai su kasar Chadi ne karkashin yarjejeniya da gwamnatin kasar.
Ya ce, gwamnatin Nigeriya ta bukaci wannan taimako kuma a cewar Mr. Warren, wannan shi ne karo na uku da ake yi irin wannan aiki idan aka hada da sauran kayayyakin aiki da suke samar da binciken hotuna ta sama, leken asiri da sauran ayyukan sirri da suka shafi tsaro ya zuwa ranar Laraban nan.
Wannan aikin da aka tsara shi, in ji kakakin, zai yi amfani da abubuwan da ake sarrafa su da kuma wadanda suke sarrafa kansu na tsaro, dangane da yadda yanayin ya bukata, sannan ya ce, babu wani shiri na gudanar da ayyukan sojojin Amurka a Nigeriya a yanzu haka. (Fatimah)