Babban kwamishinan MDD dake cikin kwamitin zabe na kasar Libya, ya musanta cewar, an tsai da takamaimar rana ta gudanar da zaben sabuwar majalisar dokokin ta Libya.
Wasu rahotanni da aka samu tun farko, sun yi ikirarin cewar, wai an tsai da ranar 25 ga watan Yuni a matsayin ranar gudanar da zaben majalisar wakilan tarayyar kasar ta Libya, to amma kuma babban kwamishinan Abdul Hakim ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, wasu rahotanni dake alaka da maganar zaben ba gaskiya ba ne, saboda sai a nan gaba ne, za'a bayyana takamaimar ranar zaben, a wani taron manema labarai na gwamnati.
Kamar dai yadda tsarin siyasa na mika mulkin kasar ya kasance, a nan gaba a cikin shekarar da muke ciki ne, 'yan kasar ta Libya za su zabi 'yan majalisar wakilan tarayyar kasar, wadanda za su maye gurbin majalisar rikon kwarya ta kasar, watau babbar majalisar kasar ta Libya. (Suwaiba)