in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yabi yadda aka gudanar da zaben Guinea-Bissau
2014-05-20 10:25:03 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayyana farin cikinsa, game da yadda aka gudanar da zagaye na biyu na zaben kasar Guinea-Bissau lami lafiya.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar a ranar Litinin, Mr. Ban ya ce, gudanar zaben na ranar Lahadi cikin kyakkyawan yanayi, ya nuna yadda al'ummar kasar ta Guinea-Bissau, suka mai da hankali ga wanzuwar yanayin zaman lafiya, da dimokaradiyya.

Har ila yau babban magatakardar MDD ya jaddada kiransa ga daukacin 'yan takarar da suka shiga zaben, da su martaba sakamakon da za a fitar a hukunce, tare da bin hanyoyin da doka ta tanada wajen warware takaddamar da ka iya biyo baya. Ya ce, nasarar wannan zabe za ta yi matukar tasiri ga burin da ake da shi, na dawo da doka da oda a kasar.

Daga nan sai ya yi kira ga daukacin al'ummar kasar da su yi amfani da wannan dama, wajen tabbatar da kyakkyawan yanayin zamantakewa, yana mai alkawarta aniyar MDD, ta baiwa kasar dukkanin goyon bayan da ya dace. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China