Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry a lokacin ziyararsa ta farko zuwa kasar Masar tun bayan hambarar da Mohammed Morsy daga mukaminsa, ya tabbatar da cewa, kasarsa za ta cigaba da marawa gwamnatin rikon kwaryar Masar baya tare da aiki da ita.
Da yake magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwwa bayan da ya gana da ministan harkokin wajen kasar na Masar Nabil Fahmy, Mr. Kerry ya yi bayanin cewa, kasar Masar wata abokiyar huldar Amurka ce, don haka Amurka ta kuduri aniyar cigaba da aiki da gwamnatin rikon kwaryar da kuma baiwa al'ummar kasar duk wani taimako da ya kamata.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi dan tsami bayan da Amurka a ranar 9 ga watan jiya na Oktoba ta sanar da dakatar da taimakon kudi har dalar biliyan 1.3 ga abokiyar huldar nata a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ministan harkokin wajen Masar Fahmy ya ce, an samu rashin kwanciyar hankali a kasar sakamakon wannan dakatarwar da Amurka ta yi.
Ziyarar Kerry a ranar Lahadin nan a Masar ita ce zangon shi na farko a ziyarar da ya fara ta kwanaki 9 a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da kasashen Turai, kuma ziyararsa ta zo a kwana daya kafin a saurari shari'ar tsohon shugaban kasar Morsy da wassu shugabannin jam'iyyar 'yan uwa musulmi su 14 da yanzu haka suke tsare bisa ga zargin tada husuma da kashe masu zanga-zanga. (Fatimah)