in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dattawar Najeriya ta bukaci Super Eagles da ta doke Bosnia-Herzegovina
2014-06-19 14:58:41 cri

A kokarin da ake yi na ganin Najeriya ta samu cancanta shiga zagaye na gaban na cin gasar kofin duniya da ake yi a Brazil, a karkashin kungiyar kwallon kafa ta duniya, majalisar dattawar Nijeriya ta yi kira a kan 'yan wasan Super Eagles na kasar, da kar su bari hakar, Bosni-Herzegovina ta kai ga nasara a gasar cin kwallon kafa na duniya.

Shugaban majalisar dattawar Najeriya David Mark, shi ne ya yi kiran a cikin wata sanarwa da ya baiwa kamfanin dillanci na Xinhua, a inda David Mark ya jaddada cewar, ya kamata 'yan wasan Super Eagles su kara kaimi a wajen wasan da za su buga da Bosni-Herzegovina a ranar Asabar mai zuwa domin su samu su doke kasar.

Mark ya bukaci 'yan wasan na Najeriya da su rike wasan da mahimmanci, kuma ya tunatar da su cewa, 'yan Najeriya na zaman jiran gnin wasan da za su yi, tare da fatan 'yan Super Eagles za su yi rawar gani domin kare mutuncin Najeriya.

Ya bukace su da su manta can-jaras din da suka yi da kasar Iran tare da kallon abin da ke tunkarar su a nan gaba. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Chile ta doke Spaniya da ci 2 da nema 2014-06-19 10:52:58
v Netherlands ta doke Australiya da ci 3 da 2 2014-06-19 10:47:40
v Croatia ta doke Kamaru da ci 4 da nema 2014-06-19 10:43:21
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China