Yan wasan kasar Chile masu cike da annashuwa, sun karya lagon Spaniya a fagen kwallon kafar duniya bayan sun fitar da ita daga gasar cin kofin duniya da ci 2 da nema a karawar da suka yi a zagayen rukuni na 2 na wasan da suka buga a ranar Laraba.
Kasar Spaniya mai kare kambu a yanzu Chile ta fitar da ita daga wasan, a inda ita kuma kasar Chile ta samawa kanta matsayi na gaba. (Suwaiba)