in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen yankin Sahel na goyon bayan sulhu a Mali
2014-04-24 09:58:21 cri

Kasashen yankin Sahel sun bayyana aniyar su, ta tallafawa zaman sulhu tsakanin 'yan adawa, da mahukuntan kasar Mali, a yunkurin da ake yin na kawo karshen rikicin siyasar kasar.

Wata sanarwar hadin gwiwar bayan taro, wadda wakilan kasashen yankin suka fitar a birnin Algiers, ta nuna cewa, an amince da kasancewar kasar Aljeriya a matsayin mai shiga tsakani, yayin da kuma daukacin kasashen za su tallafa wajen jan hankalin 'yan tawaye, su amince da shiga tattaunawar da tuni aka fara a birnin Algiers.

Da yake karin haske don gane da wannan lamari, ministan wajen kasar Algeriya Ramtane Lamamra, ya ce, babban burin da aka sanya gaba shi ne tabbatar da iko tare da hadin kan al'ummar kasar ta Mali.

Taron dai na ranar Talata ya samu halartar kusoshin gwamnatocin kasashen Mali, da Aljeriya, da Nijar, da Burkina Faso da kuma Chadi. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China