Karamin sakatare janar na MDD Jan Eliasson ya bayyana goyon bayansa a ranar Litinin kan wani ra'ayin kungiyar tarayyar Afrika AU na kara yawan sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD da ninki uku a kasar Somaliya zuwa sojoji dubu arba'in da biyar maimakon sojoji 17551 da ake da su a halin yanzu. Gwargwado shi ne na kara yaki da annobar ta'addanci a wannan kasa da ma gabashin Afrika bayan masu kaifin ra'ayin addinin islama na kungiyar Al-Shabaab ta kasar Somaliya da ta kai wani kazamin harin kunar bakin wake a ginin kasuwanci na Westgate a Nairobi, babban birnin kasar Kenya a ranar 21 ga watan Satumba.
Da yake magana bayan wata ziyarar aikin da ta kai shi a kasashen Kenya da Somaliya, jami'in na MDD ya bayyana kara yawan sojojin MDD a Somaliya da kuma dukufa ga cigaban harkokin tsaro na cikin gida na kasar da za su taimaka wajen kyautata kokarin da ake na samar da zaman lafiya a Somaliya.
Mista Eliasson ya nuna cewa, zai gabatar da wannan bukata ta kungiyar AU ga kwamitin tsaro na MDD a ranar Laraba.
Kwamitin zai iyar daukar matakin kara karfin jami'an tsaron kasar Somaliya da na tawagar sojojin kungiyar AU a kasar Somaliya wato AMISOM. (Maman Ada)