Gwamnatocin kasashen Zambiya da Zimbabwe sun cimma ra'ayin kafa wani tsarin takardar Visa ta hadin gwiwa domin kara yawan zuwan masu yawon bude ido daga kasashen waje tsakanin kasashen biyu dake makwabtaka da juna, in ji wata sanarwa da ofishin ministan yawon bude da al'adun kasar Zambiya ya fitar a ranar Alhamis.
Ministan yawon bude ido da al'adun kasar Zambiya, Jean Kapata ya tabbatar a cikin wata sanarwa cewa, kasashen biyu sun dauki niyyar kaddamar da wani tsarin takardar Visa ta hadin gwiwa tsakaninsu.
A cewar wannan sanarwa, kasashen biyu sun amince kafa wani tsarin takardar Visa ta hadin gwiwa a yayin wani taron ministocin dake kula da harkokin yawon shakatawa a lokacin bikin baje kolin yawon bude ido da aka gudanar a birnin Durban na kasar Afrika ta Kudu a makon da ya gabata. (Maman Ada)