Ma'aikatar kiwon lafiya ta Najeriya, wace ke Afrika ta yamma, ta bayyana cewar, adadin wadanda suka rasu ya karu ya zuwa mutane 20, a sakamakon harin da aka kai kwanan baya a garin Nyanya.
Ma'aikatar lafiya ta ce, daya daga cikin wadanda aka kwantar a asibitin Asokoro ya mutu, kuma wadanda suka jikkata sun kai 85.
Ma'aikatar ta ce, akwai sauran wadanda harin bam din ya shafa da ba'a san sunayensu ba a cikin kundin adadin gwamnati, domin an ce, sun je asibiti suka sama wa kansu magani saboda ba su samu rauni sosai ba.
Ministan lafiya na Najeriya Onyebuchi Chukwu, da kuma karamin ministan ma'aikatar lafiya, Khaliru Alhassan sun ziyarci asibitin domin jajantawa wadanda Allah ya tserar da rayukansu, kuma har yanzu suna jinya a asibitin. (Suwaiba)