Jam'iyyar ANC ta Afrika ta Kudu, wacce ke rike da gwamnatin kasar, ta nuna damuwarta a game da wani yajin aiki a bangaren ma'adinin karfen platinum.
Kakakin jam'iyyar ta ANC, Zizi Kodwa ya ce, yajin aiki yana tasiri sosai a kan tattalin arziki na cikin gida, da kuma na duniya baki daya, har ma da masu saka jari 'yan kasar waje, yajin aikin na ci masu tuwo a kwarya.
Kakakin jam'iyyar ta ANC, yana jawabi ne bayan wasu kamfanoni biyu na kasashen waje, masu auna tattalin arzikin kasashe, suka nuna cewar, alkalumansu ya nuna cewar, tattalin arzikin kasar ta Afrika ta Kudu ya yi kasa. (Suwaiba)