Babban sakataren majalisar dinkin duniya, mista Ban Ki-moon ya isa ranar Talata a birnin Juba a cikin wata ziyarar aiki ta yini guda a kasar Sudan ta Kudu, sabuwar kasar nahiyar Afrika dake fama da tashen-tashen hankali da yake-yake tsakanin bangaren shugaban kasar Salva Kiir da na tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.
Mista Ban zai tattauna tare da shugaba Kiir da kuma shugabannin kungiyoyin fararen hula na kasar, a cewar wata sanarwa ta tawagar MDD dake kasar Sudan ta Kudu.
Haka zalika, mista ya cigaba da rubanya kiraye-kiraye ga shugabannin Sudan ta Kudu wajen bullo da wata mafitar siyasa da kuma kawo karshen zubar da jini ba tare da wani sharadi ba. (Maman Ada)