in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ba da rahoton barkewar tashin hankali a Sudan ta Kudu
2014-06-11 13:33:23 cri

Tawagar MDD a kasar Sudan ta Kudu UNMISS na sa ido a kan tattaunawa ta musamman ta kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afirka IGAD da aka bude jiya Talata ranar 10 ga wata a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce, an samu rahoton karan manyan bindigogi daga yankin Upper Nile, bangaren tsibirin Jazeera, a ranar Litinin, kuma wasu manyan jami'ai na jihar Unity suna isar da sakonni na neman tada hankali ta kafar gidan rediyon Bentiu.

Tawagar ta MDD ta yi allah wadai da amfani da gidan rediyon, wajen isar da sakonni dake rarraba kawunan jama'a, kuma hakan na kawo cikas wajen daidaita rikici. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China