in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kara tura dakaru a kasar Sudan ta kudu
2014-05-15 10:08:26 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke aiki a kasar Sudan ta Kudu (UNMISS) ta ce, ana tura dakarun gwamnati da wadanda ke goyon bayan gwamnatin zuwa arewacin jihar Unity.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a hedkwatar MDD da ke birnin New York na kasar Amurka. Ya ce, harbe-harbe da aka yi a safiyar ranar Laraba a birnin Bentiu da Rubkona ya tilasta rufe filin saukar jiragen saman wurin na sa'o'i da dama, duk da cewa a baya yanayi ya inganta.

UNMISS ta yi allahwadai da kakkausar murya kan yadda ake sace kayayyakin kiwon lafiya da abinci, inda ta yi kira ga dukkan bangarori, da su martaba tare da kare kayayyaki da jami'an lafiyan da ke aiki, marasa lafiya da kuma wadanda suka ji rauni.

Sama da fararen hula 23,000 ne yanzu haka ke samun mafaka a sansanomin MDD da ke Bentiu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China