Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU a jiya Litinin ta yi Allah wadai da harin da aka kai a kan babban birnin kasar Najeriya, Abuja.
Shugabar hukumar kungiyar Nkosazana Dlamini-Zuma ta nuna takaicinta a game da harin bam din da aka kai, a safiyar Litinin a wajen Abuja, kamar dai yadda wata sanarwar kungiyar ta bayyana.
Shugabar AU ta nuna rashin jin dadinta da harin na ta'addanci, a inda ta mika ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya rutsa da su, da kuma jama'a da gwamnatin Najeriya.
Shugabar ta jaddada goyon bayanta ga Najeriya a kan kokarin da take yi na magance matsalar ta'addanci.
Ta yi kira ga kasashen Afrika da su dauki matakai tare domin magance wannan matsala, kamar dai yadda wasu dokoki na Afrika da na duniya suka zayyana. (Suwaiba)