in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon harin ta'addanci a Najeriya ya hallaka mutane 20
2014-05-27 10:59:30 cri

Aka kashe a kalla mutane 20 a wani kauyen dake nesa da jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya a ranar Lahadin da ta gabata a yayin da wasu mutane dauke da makamai da ake zargi da 'yan Boko Haram suka kai musu hari ta hanyar luguden wuta, in ji wata majiyar soja a ranar Litinin.

Adadin zai iya karuwa dalilin yawan mutanen da suka jikkata a wannan hari, in ji wani babban ofisa da ya bukaci a sakaya sunansa.

Jami'in ya bayyana cewa, maharan sun afkawa kauyen a cikin wata mota kafin su fara luguden wuta kan mazauna kauyen wadanda yawancinsu manoma ne da kananan 'yan kasuwa. Harin da aka shirya shi sosai, ba mu yi tsammanin wannan zai faru ba domin babu wanda ya sanar da mu, in ji wannan majiya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China