Rahotanni daga jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya na cewa, wasu 'yan bindiga sun hallaka a kalla mutane 83, sakamakon hare-haren da suka kaiwa wasu kauyukan jihar uku masu makwaftaka da kasar Kamaru.
Wata majiyar jami'an tsaron tarayyar Najeriyar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, 'yan bindigar sun kaiwa kauyukan Attagara, da Agapalawa da kuma Aganjara dake karamar hukumar Gwoza hari ne a ranar Talata, amma sai a ranar Laraba rahoton aukuwar lamarin ya isa Maiduguri, fadar gwamnatin jihar, sakamakon matsalar layukan sadarwa da ake fama da ita.
Wannan ne dai hari na biyu da al'ummar kauyen Attagara suka fuskanta a baya bayan nan, inda kwanaki uku da suka gabata, aka kaiwa wata majami'a dake garin hari wanda ya janyo mutuwar mutane 9.
A ranar Alhamis din makon jiya ma wasu mahara sun kashe mutane 32 a wani kauye dake jihar ta Borno mai makwaftaka da kasar Kamaru. (Saminu)