in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi bikin cika shekaru 10 da kafa kwamitin tsaronta
2014-05-26 12:17:29 cri

Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta yi murnar zagayowar shekaru goma da kafuwar kwamitin tsaronta wanda ke gudanar da aikin samar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar. Kungiyar ta AU ta ce, wannan biki na kungiyar zai ba da daman da ya dace ga majalisar, tare da gano kalubale da kuma hanyoyi na ci gaba da zummar bunkasa zaman lafiya mai dorewa a daukacin Afrika.

Kungiyar tarayyar kasashen Afrika ta ce, duk da yake cewar, shekaru goma da ta yi, an yi abubuwa da dama, har yanzu akwai karin gudumuwar da za'a iya bayarwa, kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU ya taimaka matuka wajen haramta fada da juna, tare kuma da sa ido a kan rikice-rikice da ke faruwa a nahiyar ta Afrika, da kuma magance rikice-rikicen da ake yi a nahiya, kamar dai yadda kungiyar ta bayyana.

Kungiyar tarayyar Afrika ta kuma ce, ta bayar da gudumuwa da zummar taimaka wajen kokarin da ake yi na kara gina kasa da ci gaba da kuma samar da zaman lafiya da zaburar da girka tsarin damokradiyyar a nahiyar ta Afrika. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China