in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi allawadai da harin ta'addanci a Urumqi na Sin
2014-05-23 15:39:34 cri

Babban sakatare na MDD Ban Ki-moon ya yi allawadai a ranar Alhamis da harin ta'addancin da aka kai wa fararen hula a wata kasuwar birnin Urumqi na jihar Xinjiang mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 31 da jikkata 94, ya bayyana cewa, babu wata hujjar aikata kisa kan fararen hula, in ji kakakin mista Ban a cikin wata sanarwa.

Mista Ban ya gabatar da ta'aziyyarsa zuwa ga iyalan da wannan hari ya rutsa da 'yan uwansu, ga jama'a da kuma gwamnatin kasar Sin tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata, in ji wannan sanarwa.

Magatakardan MDD ya kara jaddada cewa, babu wata hujjar farma fararen hula, shi kuma bayyana fatansa na ganin an gurfanar da masu hannu kan wannan hari gaban kotu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China