Jam'iyya mai mulki a kasar Afrika ta Kudu, ANC tana kan lashe sakamakon zabe mai zuwa da rinjaye, kashi biyu bisa ukku, a zaben kasa da za'a yi a ranar 7 ga watan Mayu, kamar yadda wani bincike da aka buga a jaridar Sunday Times, wacce ke fitowa a ranar Lahadi ya nuna.
Wannan bincike da aka yi ya gano cewar, akwai alamun dake nuna cewar, jam'iyyar ta ANC za ta lashe kashi 65.5 bisa dari na goyon bayan masu kada kuri'a daga cikin kusa kashi 74.5 bisa dari na yawan mutanen da ake sa ran za su fito su kada kuri'a. Wannan hasashe ya banbanta a inda ya nuna cewa, babbar jam'iyyar dake adawa da ANC, Democratic Alliance ita ana sa ran za ta sami kashi 23.1 bisa dari. A zaben shekara ta 2009, jam'iyyar ta Democratic Alliance ta samu kashi 16.7 bisa dari na kuri'un da aka kada a waccan shekarar.
Wannan hasashen da aka yi na jam'iyyar ta ANC, mai mulki a kasar ta Afrika ta Kudu ya nuna ragowar angizon jam'iyyar idan an kwatanta da ta samu kashi 65.9 bisa dari a zaben shekara ta 2009, kuma wannan sakamakon ya yi kusan daidai da sauran bincike dake nuna cewar, jami'yyar ta ANC, za ta samu rinjaye ne da kashi 60 bisa dari.
Shi dai wannan bincike da aka yi ya kuma nuna cewar, yawancin masu kada kuri'a na jam'iyyar ta ANC mai mulkin kasar, ba su yi amanna da cewa, ya kamata a rike jam'iyyar ta ANC, da laifin wani abin kunya da ya shafi shugaban kasar ba, Jacob Zuma, wanda ke fuskantar adawa, saboda zarginsa da aka yi na cewar, an aikata ba daidai ba da kudaden jama'a, a yayin da ya aiwatar da wani gini ya daga darajar gidan kansa dake Nkandla, a yankin KwaZulu-Natal. (Suwaiba)