Jam'iyya mai mulki a kasar Afrika ta Kudu ANC a Talatan nan 20 ga wata ta sanar da sunayen kantomominta a gundumomi 8 da take mulkin su.
Sanarwar ta zo ne bayan da jam'iyyar ta yi wani taro na musamman na majalissar zartarwarta a ranar Litinin a birnin Pretoria.
Wannan zama na majalissar zartarwa na musamman ya biyo bayan wani taro ne na manyan jami'an jam'iyyar da kuma majalissar gudanarwarta da suke shirin mika 'yan takararsu na wadannan mukamai a wadannan gundumomi dake karkashin mulkin ANC. (Fatimah)