in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya za ta gurfanar da mutane 5 gaban kuliya bisa zarginsu da hannu a harin Nairobi
2013-10-30 10:16:33 cri

Rundunar 'yan sandan kasar Kenya ta bayyana cewa, za ta gurfanar da wasu mutane 5 gaban kuliya, bisa zarginsu da hannu a harin nan da aka kaddamar a cibiyar cinikayyar Westgate dake Nairobi, babban birnin kasar.

Daraktan sashen binciken manyan laifuka na rundunar Ndegwa Muhoro ne ya bayyana wa manema labaru hakan, ranar Talata a birnin Nairobi.

Muhoro ya kuma ce, za su fidda takardar sammancen cafke karin wasu mutane biyu da ake zargi da hannu cikin wancan hari na ranar 21 ga watan Satumbar da ya gabata.

Cikin mutanen 5 da za a gurfanar gaban kotun, har da wani matashi 'dan shekaru 23 mai suna Hassan Abdi Dhuhulow, wanda Muhoro ya ce, haifaffen kasar Somaliya ne, wanda ya yi kaura zuwa Norway. A baya ma dai Dhuhulow ya taba kubuta daga zargin kisan wani 'dan jaridar kasar Somaliya mai suna Hassan Yusuf Absuge.

Tuni dai jami'an rundunar 'yan sandan kasar Norway suka fara gudanar da wani bincike, domin tabbatar da gaskiyar zargin da ake yiwa Dhuhulow, na kasancewa cikin wadancan mahara.

Idan dai za a iya tunawa, harin na cibiyar kasuwancin Westgate da ya sabbaba shafe kwanaki 4 ana arangama tsakani maharani da 'yan bindiga, ya haddasa rasuwar a kalla mutane 67, baya ga wasu kimanin mutane 175 da suka jikkata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China