Shugaban jamhuriyar kasar Congo Denis Sassou-Nguesso, mataimakin darektan ofishin yada labaran majalisar gudanarwar Sin Wang Guoqing, jakadan Sin da ke kasar Congo Guan Jian, wasu ministocin kasar Congo, har ma da wasu jakadun wassu kasashen dake kasar Congo sun halarci bikin bude aikin da aka yi a cikin harabar majalisar dokokin kasar Congo.
A jawabinsa wajen bikin, mataimakin darektan ofishin yada labaran majalisar gudanarwar Sin Wang Guoqing ya bayyana cewa, an fara aikin "fahimtar Sin" a jamhuriyar kasar Congo kafin sabon shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a kasar. Ana sa ran cewa, al'ummomin kasar Congo za su samu cikakken fahimta game da kasar Sin bisa fannoni daban daban ta aikace-aikacen da dama da za a shirya, misali, wasan kwaikwayo, nune-nunen bidiyo, intabiyun kafofin watsa labarai, kafuwar dakin nunin harkokin Sin da dai sauransu.
Ministan ma'aikatar kula da harkokin labarai da dangantakar majalisar dokokin kasar Congo(Brasseville) ya bayyana a wajen bikin cewa, al'adun kasar Sin na da dogon tarihi, kuma ya zuwa shekarar 2014, za a cika shekaru 50 da aka kulla dangantakar diflomasiya tsakanin kasashen Sin da kasarsa, don haka, ziyarar da shugaban kasar Sin zai yi a kasar Congo(Brasseville) za ta karfafa zumuncin tsakanin kasashen biyu, da kuma inganta cudanyar al'adun tsakaninsu.
Ban da wannan kuma, a daren wannan rana, 'yan wasan fasahar tawagar wasan kundunbala ta kasar Sin sun nuna wasannin gargajiyar Sin da suka hada da wake-wake da raye-raye, wasan dabo, da kuma wasan kundunbala, wadanda suka kayatar da baki sosai a wurin. (Maryam)