in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta tashi zuwa Brazil
2014-06-10 09:39:52 cri

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta shirya barin kasar Amurka zuwa Brazil a Talatar nan, gabanin bude gasar cin kofin duniya da za a fara ranar Alhamis.

Wata sanarwa da kakakin hukumar kwallon kafa ta Najeriyar Ademola Olajire ya fitar, ta tabbatar da cewa, kungiyar ta Super Eagles za ta baro birnin Miami na kasar Amurka zuwa birnin Sao Paulon kasar Brazil, kafin kuma daga bisani ta isa masaukin su dake otel din Campiness, a wajen birnin na Sao-Paulo.

Yayin gasar ta bana dai Super Eagles za ta bude wasanta ne da kasar Iran cikin rukuni na 6 a ranar 16 ga watan nan, kafin karawarta ta biyu da Bosnia-Herzegovina a ranar 21 ga wata. Kaza lika kungiyar za ta fafata da kasar Argentina a wasa na uku ranar 25 ga watan nan na Yuni.

Rahotanni dai sun ce, tuni shugaban hukumar kwallon kafar kasar ta NFA Aminu Maigari, ya isa birnin Sao Paulo, domin halartar babban taron hukumar FIFA karo na 64, wanda aka shirya gudanarwa a ranekun 10 da 11 ga watan nan. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China