Wani wakili na musamman daga kungiyar tarayyar kasashen Turai EU ya ziyarci kasar Libya jiya Lahadi, a wani kokari na taimakwa kasar gano bakin zaren, tabarbarewar mummunan rikici na siyasar kasar, a inda kuma wakilin na musamman, ya yi kira a kan 'ya'yan kasar ta Libya da su girmama hukumomin kasar.
Wakili na musamman na EU, Bernardino Leon, ya ce, kungiyar tarayyar Turan ta yi kira a kan daukacin bangarorin da abin ya shafa, da su yi biyayya ga kasarsu, a inda ya kara da cewar, akwai bukatar gwamnatin ta Libya ta maido da martabar kasar ta, ta hanyar yaki da ta'addanci tare kuma da gina kakkarfar kasa.
Jawabin na Leon, ya zo ne 'yan kwanaki bayan da manjo janar Khalifa Haftar mai ritaya, ya kaddamar da wadansu hare-hare da sunan yin waje da 'yan ta'adda, a kan majalisar dokokin kasar dake bisa mulki a yanzu.
To amma 'yan majalisar dokokin Libya sun yi allah wadai da hare-hare na Haftar, a inda ta kira hare-haren a matsayin wani juyin mulki. (Suwaiba)