Shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a jamhuriyar demokaradiyyar Congo DRC (MONUSCO), mista Martin Kobler ya yi allawadai da tashe-tashen hankali tsakanin kabilu a gundumar Kudancin Kivu, dake gabashin kasar DRC-Congo, tare da yin kira da a kawo karshen wannan rikici nan take.
A cikin daren ranar Jumma'a zuwa ranar Asabar ne, wani kazamin fada ya barke tsakanin kabilar Bafuliru da kabilar Barundi ta Banyamulenge a yankin Uvira dake kudancin Kivu.
Wadannan tashe-tashen hankali na kabilu sun janyo asarar rayuka. Kimanin mutane talatin suka kwanta dama a yayin wasu da dama suka jikkata, in ji tawagar MONUSCO.
A kasar ta DRC-Congo, tawagar MONUSCO na tallafawa rundunar sojojin kasar Congo (FADRC), da kuma hukumonin yankunan kasar domin maido da zaman lafiya.
Sojojin MDD sun kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibitocin kasar domin ba su jinya. (Maman Ada)