in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta karfafa dangantakar cinikayya da Namibia
2013-02-22 14:20:53 cri

Ministan ma'aikatar cinikayyar kasar Sin Chen Deming, ya bayyana aniyar kasarsa, don gane da bunkasa hadin gwiwar cinikayya da kasar Namibia.

Ministan wanda ya bayyana hakan ga firaministan kasar ta Namibia Hage Geingob, yayin da tawagar 'yan kasuwar Sin ta kai ziyarar kwanaki 3 kasar, ya ce, hakan zai taimaka wajen rage matsalar karancin ayyukan yi, da bunkasa kafuwar kananan masana'antu, maimakon dogaro ga sarrafa kayan da masana'antu ke amfani da su, baya ga batun samar da damar fidda hajojin kasar ta Namibia zuwa kasar Sin.

Yayin ziyarar girmamawa da tawagar ta kai fadar tsohon shugaban kasar Sam Nujoma, da shugaba mai ci Hifikepunye Pohamba, da ma firaminista Geingob, Chen ya jinjinawa jagororin, saboda yunkurinsu na tabbatar da zaman lafiya da lumana a kasar ta Namibia, yana mai cewa, Sin na mai da hankali matuka ga muhimmancin da kasar ke da shi.

Bugu da kari, Chen ya gana da ministan cinikayya da masana'antu Calle Schlettwein, da kuma daraktan hukumar tsare-tsaren kasar Tom Alweendo, inda suka sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa don gane da ayyukan ci gaba da aka tsara gudanarwa a madadin kasashen biyu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China