Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta yi suka da babbar murya game da harin ta'addanci da aka kai a birnin Jos dake kasar Nigeriya. A cikin wata sanarwa da aka fitar, shugabar kungiyar Madam Nkosozana Dlamini-Zuma ta soki wannan tagwayen hare-haren da aka kai a tsakiyar kasuwar birnin na Jos a ranar Talata, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da goma, sannan wadansu da yawa kuma suka jikkata.
Madam Zuma ta bayyana jimamin kungiyar a kan wannan tashin hankali da kuma ta'aziyyarta ga gwamnati, al'umma da kuma iyalan wadanda suka rasu, tare da fatan wadanda suka ji rauni za su samu gwarin gwiwwa, su kuma ji sauki cikin sauri.
Shugabar ta kuma jaddada goyon bayan kungiyar ta AU ga Nigeriya a kokarin da take yi wajen yaki da ta'addanci. A don haka ne ma take maraba da shawarwarin da aka cimma a karshen taron shugabannin hukumomin tsaro karo na biyar na kasashen yankin Sahel da aka kammala a Ouagadougou a watan Mayun nan da suka ba da damar samar da wani shiri da za'a hada hannu tare domin yakar kungiyoyin ta'addanci a yankin baki daya da suka hada da Boko Haram.
Madam Nkosazana Dlamini-zuma daga nan sai ta kara jaddada bukatar dake akwai ga kasashe mambobin kungiyar ta AU tare da sauran kasashen duniya da su kara kokari wajen yakar ta'addanci. (Fatimah)