in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga mahukuntan Ghana da su aiwatar da manufofin bunkasa yankunan talakawa
2014-06-04 09:59:03 cri

An yi kira ga mahukuntan kasar Ghana da ma na sauran kasashen Afirka, da su zage damtse wajen aiwatar da manufofin bunkasa yankunan da ke da rinjayen marasa karfi.

Babban jami'in bankin duniya mai lura da harkokin da suka jibanci tattalin arziki Francisco Ferreira ne ya gabatar da wannan shawara, yayin da yake jawabi gaban mahalarta wani taron yini guda, wanda bankin na duniya ya dauki nauyin shiryawa.

Ferreira ya ce, ya lura kwarai da karancin ci gaba, tare da babban gibi dake tsakanin birane da kauyukan kasar ta Ghana, wanda hakan a cewar sa, na da mummunan sakamako a nan gaba. Don haka Ferreira ya ja hankalin mahukunta, da su rungumi manufofin yaki da talauci, da habaka ci gaban yankunan karkara, tare da alkinta dukiyar kasa, domin magance gibin dake tsakanin mawadata da masu kananan karfi.

Shi ma a nasa jawabi, Santiago Herrera, daya daga kusoshi a bankin duniyar, cewa ya yi, za a kai ga cimma manufar bunkasa kasar ta Ghana ne kawai, idan har aka fadada hanyoyin samar da ci gaba, maimakon dogaro kacokan kan kudaden da ake samu daga cinikin albarkatun man fetir.

Wakilai mahalarta taron dai sun yabawa kasar ta Ghana, bisa namijin kokari da ta yi, a fannin inganta tsarin dimokaradiyya, da kuma gudummawar da jam'iyyun gama kai ke bayarwa, wajen kyautata tsarin gudanarwar kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China