in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya bukaci a daukar matakan wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu
2014-05-28 09:45:47 cri

Kwamitin tsaron MDD ya yi kira ga tawagar wanzar da zaman lafiya ta UNMISS, da ta dauki dukkanin matakan da suka wajaba, wajen tabbatar da cimma kudurorin aikin ta a kasar Sudan ta Kudu.

Wani kudiri da ya samu amincewar daukacin wakilan kwamitin na tsaro su 15, ya yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Janairu, tsakanin sassan kasar da ba sa ga-maciji da juna, da ma yarjejeniyar baya bayan nan da sassan biyu suka sanyawa hannu.

Har ila yau kudirin ya ja hankalin sassan biyu da su dukufa wajen aiwatar da yarjejeniyar ba tare da bata lokaci ba, tare da daukar matakan da suka wajaba, kan wadanda ke burin yiwa shirin wanzar da zaman lafiyar makarkashiya.

Bugu da kari, kwamitin tsaron ya bukaci tawagar wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudun da ta ci gaba da ayyukan da suka shafi ba da kariya ga fararen hula, da sanya ido kan hakkokin bil'adama, share fagen shigar da kayan agajin jin kai, da kuma marawa shirin dakatar da rigingimu baya.

Hakan dai ya zo gabar da kwamitin ya amince da tsawaita wa'adin aikin tawagar ta UNMISS zuwa 30 ga watan Nuwambar wannan shekara da muke ciki. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China