Shugaban kasar Benin Boni Yayi ya ba da afuwarsa a ranar Laraba da yamma da a saki duk wadanda ake zargi da hannu a cikin yunkurin kashe shi, da kuma wadanda ake zargi da neman gurbata zaman lafiyar kasa, inda ya ba da umurnin a saki duk wadanda ake tuhuma.
Na dauki wannan mataki bisa imanina da 'yancina na yin afuwa. Wannan afuwa ta shafi Patrice Talon, Boco Olivier da kuma duk wadanda ake tsare da su dake da hannu wajen hada kai da kungiyoyin 'yan ta'adda da neman kashe shugaban kasa ta hanyar ba shi abinci mai guba, da kuma wadanda ake zargi da neman kawo baraka ga kasa, in ji shugaban kasar Benin Boni Yayi a cikin wani jawabinsa zuwa ga 'yan kasa. (Maman Ada)