Manyan kungiyoyin kwadago biyu na bangaren shari'a a kasar Benin, sun fara wani yajin aikin kwanaki uku na kashedi a ranar Talata, bayan sun ajiye wata takardar hadin gwiwar shiga yayin aiki a 'yan kwanakin da suka gabata.
Kungiyar alkalan kasar Benin (UNAMAB) da kungiyar ma'aikatan shari'a da makamantansu na kasar Benin (SYNATRAJAB) sun gabatar da jerin koke-kokensu da suka shafi tabbatar da 'yancin gudanar da aikinsu, tsaron lafiyar manyan alkalai da kuma neman kyautatuwar zaman rayuwa da aiki na ma'aikatan shari'a a kasar Benin.
Kungiyoyin biyu sun baiwa gwamnatin Benin lokaci sau da dama domin ta biya bukatunsu. (Maman Ada)