Rahotanni daga kasar Afirka ta Kudu sun tabbatar da cewa, 'yan majalissar dokokin kasar sun amince da zaben shugaba Jacob Zuma, a matsayin wanda zai sake shugabantar kasar nan da wasu shekaru biyar masu zuwa.
Kafin hakan dai sai da babban mai shari'ar kasar Mogoeng Mogeng ya yi watsi da korafin da jam'iyyar adawa ta AD ta gabatar, sakamakon abin da ya kira koke maras dalili.
Yanzu haka dai shugaba Zuma zai ci layar kama aiki a ranar Asabar 24 ga watan nan, a wani bikin rantsuwa da za a shirya gudanarwa a birnin Pretoria.
Kaza lika jam'iyyar ANC mai mulkin kasar ta mika sunan Baleka Mbete, a matsayin wanda take fatan ya dare kujerar kakakin majalissar dokokin kasar, inda zai maye gurbin Max Vuyisile Sisulu. Hakan dai na zuwa ne bayan da aka rantsar da sabbin 'yan majalissar dokokin kasar su 400 a ranar Laraba. Kimanin kaso 42 na 'yan majalissar dokokin kasar dai mata ne. (Saminu)