in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cibiyoyin ba da lamuni sun jinjinawa ci gaban da Habasha ta samu
2014-05-15 09:44:31 cri

A karon farko, cibiyoyin ba da lamuni na Moody's, da Fitch da kuma S&P, sun amince da irin ci gaban da kasar Habasha ta samu ta fuskar bunkasar tattalin arziki.

Ministan kudi da bunkasar tattalin arzikin kasar ta Habasha Sufian Ahmed ne ya bayyana hakan a jiya Laraba, lamarin da a cewarsa zai baiwa masu ruwa da tsaki, musamman masu bukatar zuba jari daga ketare cikakkun bayanai da za su bukata, game da matsayin hada-hadar cinikayya a kasar.

Ahmed ya ce, gwamnatin kasar ce ta samarwa cibiyoyin dukkanin bayanan da suke bukata, kafin daga bisani su tantance, su kuma fitar da sakamakon.

Ya ce, sakamakon na yanzu ya nuna matsayin kasar ya kai ta iya shiga a dama da ita a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta kasa da kasa, ko da yake a cewarsa, gwamnati ba ta kai ga yanke shawara kan hakan ba.

Baya dai ga batun fadadar tattalin arzikin Habasha, wannan sakamako ya kuma nuna yadda yaduwar arziki tsakanin sassan kasar ya kyautata, baya ga raguwar talauci da aka samu cikin shekaru 10 da suka gabata.

Kaza lika kasar ta cimma nasarori na muradun karni ko MDGs, fannonin da suka hada da na yaki da fatara, da rage mace-macen kananan yara. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China