in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya na shirin ba da sabbin lasisin hakar danyen mai
2014-04-28 09:56:26 cri

Nan gaba kadan gwamnatin kasar Kenya za ta ba da sabbin lasisin izinin hakar danyen mai, a wani shiri da ake fatan aiwatarwa da zarar an kammala aiki kan sabuwar dokar hakar man.

A cewar wani babban masanin binciken karkashin kasa na ma'aikatar makamashin kasar Hudson Andambi, ya zuwa yanzu cikin rijiyoyin man kasar 46, 41 ne kadai ake fitar da mai daga gare su.

Andambi ya ce, babban bankin duniya na taimakawa kasar wajen gudanar da nazari, kan ainihin halin da sashen manta ke ciki, gabanin babban taron nune-nunen al'barkatun mai na kasashen dake gabashin Afirka. Ana kuma sa ran taron na yini uku, zai baiwa kasashen yankin damar tattaunawa kan hanyoyin inganta hakar mai da dangoginsa.

Kafin babban zaben kasar na shekarar 2013 ne dai, gwamnatin kasar ta umarci a dakatar da hakar mai daga sabbin rijiyoyin dake kasar, wadanda mafi yawancin su ke da lasisi da aka bayar, ta hanyar cimma yarjejeniyar kai tsaye da gwamnati.

Sai dai karkashin sabuwar dokar da ta shafi wannan batu, ana fatan cefanar da rijiyoyin man ne ga tayi mafi tsoka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China