Yankin dake kewaye da jamhuriyar demokradiyya ta Congo DRC yana fuskantar wani sabon yanayi na tangadawa, in ji manzo ta musamman ta MDD a ranar Litinin din nan lokacin zaman kwamitin tsaro majalissar.
Mary Robinson, manzo ta musamman ga magatakardar MDD a yankin Great Lakes, ta shaida wa kwamitin mai mambobi 15 ta sakon bidiyo daga babban birnin kasar Kinshasa cewar, yanayin tabbaci da aka samu sanadiyar murkushe 'yan tawayen M23 da kuma rattaba hannu a kan yarjejeniyar Kampala ya gushe.
Kasar jamhuriyar demokradiya ta Congo dai ta rattaba hannu na zaman lafiya, ita da kungiyar 'yan tawaye ta M23 a watan jiya a gaban shugabannin yankin a Nairobi, babban birnin kasar Kenya, sai dai sabon salon tashin hankalin da ya kunno kai yanzu shi ne mummunan harin da wata kungiyar 'yan tawaye Allied Democratic Forces ADF ta kai a gabashin kasar, kaman fadan da yanzu haka ake yi a kasar Afrika ta Tsakiya da kuma Sudan ta Kudu.
Madam Mary Robinson ta ce, zaman lafiya, tsaro da hadin gwiwwa ga kasar da kuma yankin ya rage wata dama da ya rage wajen samun dauwamammen zaman lafiya, tsaro, hadin gwiwwa da cigaba a yankin na Great Lakes. (Fatimah)