Gwamnatin kasar Somaliya ta yi kira a ranar Litinin ga mayakan sa kai na kungiyoyin daban daban dake hannu a cikin yake-yaken da ake a yankin kudancin kasar na Bas Shaebelle da su dakatar da bude wuta nan take, a cewar wata sanarwar gwamnatin kasar. Kusan mutane goma ne aka kashe yayin da wasu da dama suka jikkata a wasu sabbin tashe-tashen hankali tsakanin mayakan wasu kungiyoyi masu gaba da juna a makon da ya gabata. Mayakan sa kan na takadama ne kan wasu yankuna masu muhimmanci dake shiyyar kudancin Mogadishu, babban birnin kasar.
Fadar faraminstan kasar Somaliya ta sanar da tura wata tawagar ministocin gwamnatin kasar a wannan shiyya domin taimaka wajen kawo karshen rikicin da kuma ba da damar yin shawarwari da sasantawa tsakanin al'ummar wannan yankin Bas Shaebelle.
Manzon musamman na MDD a kasar Somaliya, Nicholas Kay ya bayyana damuwarsa kan wadannan tashe-tashen hankali, tare da yin kira da a kawo karshen rikicin. Haka kuma mista Kay ya yi kira ga bangarorin da rikicin ya shafa da su ba da hadin kai ga tawagar zaman lafiya da gwamnatin kasar ta tura a yankin. (Maman Ada)